(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa ya na dauke da sako na musamman ga kasashen duniya dangne da tabbatar da zaman lafiya a yankin gabasa ta tsakiya a jawabin da zai gabatar a gaban shuwagabannin kasashen duniya a babban zauren majalisar dinkin duniya nan gaba.
Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban Ruhani yana fadar haka ne bayan isarsa birnin New Yorka na kasar Amurka don halattar taron shekara-shekara na 74 na babban zauren majalisar a jiya Litinin.
Banda haka shugaban ya kara da cewa akwai sako na kasar mutanen kasar Iran ga kasashen duniya dangane da mummunan yakin tattalin arziki, ko ta’addancin tattalin arziki wanda gwamnatin kasar Amurka da dorawa kasar.
Kafin ya bar Tehran zuwa birnin New York dai shugaba Ruhani ya bayyana cewa sakonnin zaman lafiya da zai bayyana su a jawabin da zai gabatar a babban zauren majalisar dinkin duniya dai yana dauke da manufofin zaman lafiya a gabas ta tsakiya, wanda ba zai tabbata ba sai tare da dauke hannun dukkan kasashen waje a yankin.
/129